An hallaka wasu daga cikin shugabanin kungiyar IS a arewacin Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i9913-an_hallaka_wasu_daga_cikin_shugabanin_kungiyar_is_a_arewacin_iraki
Harin da Jiragen yakin kasar Iraki suka kai a Garin Mosil ya yi sanadiyar hallaka wasu daga cikin shugabanin IS
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 21, 2016 01:15 UTC
  • An hallaka wasu daga cikin shugabanin kungiyar IS a arewacin Iraki

Harin da Jiragen yakin kasar Iraki suka kai a Garin Mosil ya yi sanadiyar hallaka wasu daga cikin shugabanin IS

A wani hari da jiragen Yakin kasar Iraki suka kai ga daya daga cikin guraren taruwar mayakan ISIS a yankin Misak dake yammacin garin Mosil, 'yan ta'adda 19 ne suka hallaka, daga cikin su har da wasu daga cikin shugabanin su.har ila yau rahoton ya ce daga cikin shugabanin ISIS din da suka hallaka har da Ayad Hamid Mahalil-jamili wanda aka fi sani da Abu Yahaya.

A wani hari kuma da Jiragen yakin Irakin suka kai jiya Assabar a yankunan kauyen Hayt dake yammacin Anbar, 'yan ta'addar IS 8 ne suka hallaka sannan kuma aka tarwatsa wasu Motocin yaki na 'yan ta'addar.

A bangare guda Kakakin Rundunar hadin gwiwa na Dakarun Irakin Yahaya Rasul ya bukaci mazauna Garin Mosil da su zauna a cikin gidajen su domin babbance 'yan ta'adda da fararen hula a yayin da  fara kai farmaki a garin domin tsarkake shi daga hanun 'yan ta'addar na ISIS.
Kakakin Rundunar Hadin gwiwar ya tabbatar da cewa su nada cikekken bayanai na guraren da 'yan ta'addar ISIS din suke a garin Mosil, domin haka babu wani abinda zai sanya damuwa a yayin da Dakarun kasar za su kai farmaki kan 'yan ta'addar.

Rasul ya ce Dakarun tsaron kasar na cikin shirye-shirye na fara kai farmaki kan 'yan ta'addar na ISIS dake garin Mosil kuma nan ba da jimawa ba za a fara wannan aiki domin 'yanto wannan yanki.