-
Jiragen Yakin Kawancen Saudiya Sun Kai Hari Kan Fadar Shugaban Kasar Yemen
Dec 05, 2017 03:03A daren jiya litinin, jiragen yakin kawancen saudiya sun yi luguden wuta kan fadar shugaban kasar Yemen a birnin San'a.
-
Syria: Harin Makamin Roka A Birnin Damascuss Ya Kashe Mutane Biyu
Dec 04, 2017 15:24Majiyar tsaro a kasar Syria ta ce 'yan tawaye sun harba makamin roka ne akan yankin Abbasiyyin da ke cikin babban birnin kasar tare da kashe mutane biyu dakuma jikkata wasu bakwai.
-
Isma'ila Haniyyah: Al'ummar Musulmi Sun Hadu Akan Batun Masallacin Kudus
Dec 04, 2017 15:22Ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta bakin shugabansa Isma'ila Haniyyah, ya yi gargadi akan shirin Amurka na maida ofishin jakadancinta zuwa Birnin Kudus.
-
Abdulmalik al-Huthy: An Murkushe Babban Makirci Akan Al'ummar Yemen
Dec 04, 2017 15:20Babban sakataren kungiyar Ansarullah wanda ya gabatar da jawabi dazu ya tabbatar da kashe Ali Abdallah Saleh sannan ya ce; Rana ce ta musamman kuma ta tarihi domin an murkushe makirci da makarkashiya
-
Bahrain: An Kai Ayatollah Sheikh Isa Qasim Asibiti
Dec 04, 2017 09:31An kai babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Qasim asibiti a safiyar yau, sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.
-
Sojojin Isr'aila Sun Yi Awon Gaba Da Masu Gadin Masallacin Quds
Dec 04, 2017 09:29Jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi awon gaba da mutane hudu daga cikin masu gadin masallacin aqsa.
-
Yemen: An Kashe Tsohon Shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh
Dec 04, 2017 09:25Rahotanni daga Yemen sun ce an kashe tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh a yau a lokacin da yake shirin tsrewa daga San'a zuwa Maariba.
-
Mayakan Huthi Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Cibiyar Nukliyar Al-Barakar Na AbuDhabi
Dec 03, 2017 15:30Mayakan huthi na kasar Yemen sun bada labarin cilla makamai masu linzami kan cibiyar makamashin Nukliya ta Al-barakat da ke birnin Abu dabi na kasar Hadaddiyar daular Larabawa.
-
Babban Sakataren Kungiyar Ansarullahi Ta Yamen Ya Yi Gargadi Kan Fitinar Da Ta Kunno Kai A Kasar
Dec 02, 2017 15:33Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi ya yi kira ga al'ummar Yamen da su fadaka kan makircin da mahukuntan Saudiyya suke kitsawa da nufin hada al'ummar Yamen fada a tsakaninsu.
-
An Gudanar Da Zanga-Zangogin Kin Jinin Gwamnati A Kasar Bahrain
Dec 02, 2017 08:17Rahotanni daga kasar Bahrain sun bayyana cewar al'ummar kasar sun gudanar da wasu sabbin zanga-zangogin kin jinin mahukuntar kasar da kuma bakar siyasar da suke gudanarwa musamman ci gaba da killace babban malamin Shi'a na kasar Sheikh Isa Qassim da gwamnatin take yi.