-
Iraki: Dakarun Sa-Kai Na Iraki Sun Fatattaki 'Yan TA'adda A yankuna Da Dama.
Oct 27, 2017 02:56Majiyar dakarun na "Hashdus-sha'abi' ta ce; sun 'yanto da garin Jabab da ke yammacin Anbar daga mamayar 'yan ta'addar Da'esh, tare da daga tutar Iraki a cikinsa.
-
Wani Dan Majalisar Dokokin Sudan Ya Ce Shigar Kasar Cikin Yakin Kasar Yamen Bai Dace Ba
Oct 26, 2017 15:20Wani dan Majalisar Dokokin Sudan ya bayyana rashin amincewarsa da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na shiga cikin rundunar kawancen Saudiyya da take yaki a kasar Yamen.
-
Pakistan : An Fitar Da Sammacin Kame Nawaz Sharif
Oct 26, 2017 07:51Kotun da ke kula da yaki da cin hanci da rashawa a Pakistan, ta bayar da sammacin kame tsohon firayi ministan kasar, Nawaz Sharif, bisa badakalar cin hanci da rashawa.
-
Sojojin Iraki Sun Kaddamar Da Hare-Haren Kwato Yankin Kasar Na Karshe Da Ke Hannun ISIS
Oct 26, 2017 02:18Sojojin kasar Iraki sun sanar da fara kaddamar da wani gagarumin hari na soji da nufin kwato yankuna na karshe da suke hannun 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) a lardin Anbar na kasar.
-
Firayi Ministan Iraki Na Ziyara A Turkiyya
Oct 25, 2017 07:49Firayi ministan Iraki, Haidar al-Abadi, ya gana da shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erodgan a wata ziyara da ya soma yau a birnin Ankara.
-
Hamas: Ba Za Mu Taba Watsi Da Makamai Ba.
Oct 25, 2017 03:21Shugaban Kungiyar Hamas a yankin Gaza Yahya Sinwar ya ce; Makamin da yake hannun kungiyar ta Hamas mallakin dukkanin palasdinawa ne.
-
An Kira Yi Al'ummar Bahrain Domin Yin Zanga-zangar Nuna Goyon Baya Ga Fursunonin Siyasa
Oct 25, 2017 03:19Kawancen 14 ga watan Fabrairu na Bahrain ne ya fitar da sanarwa wacce ta kunshi gayyatar mutanen kasar zuwa Zanga-zanga a ranar juma'a mai zuwa.
-
Yemen: Dakarun Sa-Kai Na Ansarullah Sun Kai Hari A Sansanonin Saudiyya Da Ke Asir.
Oct 25, 2017 03:13A jiya talata ne sojojin Yemen da kuma dakarun sa-kai na Ansarullah suka kai harin da manyan bindigogi a sansanonin Saudiyya na al-majazah da Riqabatul Hanjar da ke gundumar Asir.
-
Masar : A shirye Mu Ke Mu Kawar Da Sabaninmu Da Iran_ Al Sissi
Oct 24, 2017 07:18Shugaba Albdelfatah Al-Sissi, na Masar, ya ce a shirye kasarsa ta ke domin kawar da sabanin dake tsakaninta da Iran.
-
Gwamnatin Rasha Ta Kore Zargin Da Shugaban Kasar Afganistan Ya Yi Kan Kasarta
Oct 24, 2017 03:03Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa: Zargin da shugaban kasar Afganistan ya yi kan kasar Rasha cewa tana goyon bayan kungiyar Taliban; zargi ne maras tushe da Rasha ba zata taba lamunta ba.