-
Iraki Tana Ci Gaba Da Mayar Da Martani Ga Sakataren Harkokin Wajen Amurka Martani
Oct 23, 2017 15:52Kakakin mayakan sa-kai na "Hashdu-sha'abai" na Iraki ya bukaci sakataren harkokin waje Rex Tilerson , ya nemi gafara akan furucinsa dangane mayakan.
-
IS Ta Kashe Mutum 116 kafin Ta Arce Daga Tsakiyar Siriya
Oct 23, 2017 07:32Kungiyar kare hakkin bil adama ta OSDH a Siriya ta ce kungiyar 'yan ta'addan IS ko Da'esh sun kashe fararen hula 116 kafin su arce daga yankin al-Qaryatayne.
-
Gwamnatin Masar Ta Jaddada Matsayinta Na Taimakawa Iraqi Kan Yaki Da Ta'addanci
Oct 23, 2017 02:55Shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi ya kara jaddada matsayin gwamnatinsa na tallafa wa kasar Iraqi a yakin da take yi da yan ta'adda.
-
Iraki: Babbar Jam'iyyar Adawa A Yankin Kurdistan Ta Bukaci A Kafa Gwamnatin Tseratar Da Mutanen Yankin
Oct 23, 2017 02:55Jam'iyyar adawa mafi girma a yankin kursdistan na kasar Iraqi ta bukaci Massoud Barazani ya sauka daga kujerar shugabancin yankin sannan a kafa gwamnatin tseratar da yakin daga halin da Barazani ya jefa shi a ciki.
-
Sojojin Iraki Sun Kwace Rijiyoyin Man Fetur 44 Da Ke Yankin Kurdawa
Oct 21, 2017 15:21Tashar telbijin din al'alam ta sanar da cewa; bayan ficewar mayakan Kurdawa na Peshmarga daga gundumar Nainawa, sojojin na Iraki sun shimfida ikonsu a rijiyoyin man fetur din 44.
-
Syria Ta Yi Allah Wadai Da Harin Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Akan Iyaka
Oct 21, 2017 15:19Ma'aikatar harkokin wajen ta Syria ta fitar da wani bayani ne da a ciki ya yi tir da harin da sojojin Isra'ila suka kai da manyan bindigogi a yankin Kunaitara.
-
Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Kurdawa
Oct 21, 2017 14:51Tashar telbijin din al'alam ta nakalto cewa; Pira ministan haramtacciyar Kasar Isra'ila yana ci gaba da nuna goyon bayansa ga kokarin ballewar Kurdawa.
-
Yemen: Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula 20
Oct 21, 2017 14:50Jiragen yakin na Saudiyya sun kai hari ne akan iyakar Gamr a gundumar Sa'adah da ke arewacin kasar.
-
Ayat. Sistani Ya Bukaci Gwamnati Da Ta Kare Kurdawan Iraki Duk Kuwa Da Sabanin Da Ake Da Shi
Oct 20, 2017 13:47Babban marja'in 'yan Shi'an kasar Iraki, Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya kirayi gwamnatin kasar Irakin da ta ba wa Kurdawan kasar kariya duk kuwa da sabanin da ya kunno kai da kuma ci gaba da kai ruwa rana da ake yi tsakanin gwamnatin Iraki da na yankin Kurdawan da suke son ballewa.
-
Kungiyar Hamas Ta Palasdinu Ta Zargi Kasar Amurka Da Tsoma Baki A Harkokin Palasdinawa
Oct 20, 2017 03:03Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa: Bukatar gwamnatin Amurka ta neman Palasdinawa su amince da halaccin haramtacciyar kasar Isra'ila, tsoma baki ne a harkokin da suka shafi al'ummar Palasdinu.