Yemen: Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula 20
Jiragen yakin na Saudiyya sun kai hari ne akan iyakar Gamr a gundumar Sa'adah da ke arewacin kasar.
Kamfanin dillancin labarun "Irna" ya ambato majiyar tsaron kasar ta Yemen na cewa; Harin ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 20, yayin da wasu biyar suka jikkata.
A arewacin birnin Sa'adah, jiragen yakin Saudiyyar sun harba makamai masu kwafsa da aka haramta amfani da su a duniya, tare da jikkata kananan yara biyar.
A jiya juma'a ma dai jiragen yakin na Saudiyya tare da sojojin hayar kasar Sudan sun kai hari a garin Medi da ke kan iyaka. Sau 20 jiragen yakin suka kai wa garin hari.
Tun a cikin watan Maris na 2015 ne dai Saudiyyar ta shelanta yaki akan al'ummar Yemen da kawo ya zuwa yanzu suka kashe fiye da mutane 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.