Oct 24, 2017 06:33 UTC
  • Gwamnatin Rasha Ta Kore Zargin Da Shugaban Kasar Afganistan Ya Yi Kan Kasarta

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa: Zargin da shugaban kasar Afganistan ya yi kan kasar Rasha cewa tana goyon bayan kungiyar Taliban; zargi ne maras tushe da Rasha ba zata taba lamunta ba.

A bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar a jiya Litinin yana dauke da cewa: Gwamnatin Rasha tana goyon bayan irin kokarin da rundunar sojin Afganistan take gudanarwa a fagen yaki da ta'addanci, kuma baya ga haka gwamnatin Rasha tana da ra'ayin ganin an bude fagen gudanar da zaman tattaunawan sulhu tsakanin gwamnatin Afganistan da kungiyar ta Taliban da nufin samar da zaman lafiya da sulhu a kasar.

Har ila yau bayanin na ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi shugaban kasar Afganistan Ashraf Ghani da ya nisanci wurga kansa cikin kangin makirci da tarkon kafofin watsa labaran kasashen yammcin Turai ta hanyar furta maganganu marassa tushe kan kasar Rasha, domin kafofin watsa labaran Turai ne suke yada zarge-zargen cewa gwamnatin Rasha tana goyon bayan kungiyar Taliban.

Wannan bayani na ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ya zo ne a matsayin maida martani kan furucin da shugaban kasar Afganistan Ashraf Ghani ya yi a jiya Litinin, inda ya zargi kasashen Rasha da Pakistan da hannu a goyon bayan kungiyar Taliban ta kasarsa ta hanyar mallaka mata makamai da kudade.  

Tags