-
Syria: Rasha Za ta Kara Yawan Hare-haren da ta ke kai wa 'Yan ta'adda
Feb 13, 2017 08:37Jaridar Nazavisimiya Gazat, ta kasar Rasha ta ce; Bude tattaunawar sulhu a Syria ba zai hana hare-haren da Rasha ta ke shirinkai wa 'yan ta'adda ba a kasar Syria.
-
Yahudawan HKI Zasu Hana Kiran Sallah A Dukkan Masallatai A Yankunan Palasdinawa
Feb 13, 2017 02:49Komitin da majalisar ministocin HKI ta kafa don hana kiran sallah a yankunan Palasdinawa da ta mamaye da su ya amine da dokar kuma mai yuwa cikin yan kwanaki masu zawa gwamnatin haramtacciyar kasar zata hana kiran salla a wadannan yankuna.
-
Sayyid Nasrallah: Ba Ma Cikin Damuwa Don Kuwa Sabon Shugaban Amurka Wawa Ne
Feb 12, 2017 13:44Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya gode wa shugaban kasar Amurka Donald Trump sakamakon yadda ya bayyanar da hakikanin yanayin Amurka wa duniya, yana mai cewa ba sa cikin wata damuwa don kuwa wawa ne ke mulkin Amurkan.
-
Jiragen Yakin Saudiyyah Sun Yi Ruwan Bama-Bamai A Gundumar Hijja A Kasar Yemen
Feb 12, 2017 03:39A daren jiya jiragen yakin masarautar Saudiyyah sun yi ruwan bama-bamai a kan gidajen jama'a a yankunan daban-daban da ke cikin lardin Hijja na kasar Yemen.
-
Iraki : Mutane 7 Sun Mutu A Yayin Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
Feb 11, 2017 12:39Rahotannin daga Iraki na cewa mutane bakwai ne suka mutu a yayin wata zanga-zanga kin jinin gwamnati a Bagadaza babban birnin kasar.
-
Afirka Ta Kudu Na Ci-gaba Da Goyon Bayan Palestine (Zuma)
Feb 11, 2017 12:09Shugaba Jacob Zuma na Afrika ta Kudu ya yi Allah wadai da ci gaba da mamayar da yahudawan Isra'ila ke yiwa al'ummar Palestinu.
-
Syria : An Sake Gayyatar Bangarorin Dake Rikici Kan Tebirin Tattaunawa
Feb 11, 2017 11:29Ma'aikatar harkokin wajen kasar Kazakstan ta ce an sake gayyatar bangaren gwamnati da 'yan tawayen Syria a wani sabon zagayen tattaunawa sulhu da za'ayi a tsakiyar watan Fabrairu nan a birnin Astana.
-
An Bukaci Tsoma bakin Babban Sakataren M.D.D. Kan Kawo Karshen Hare-Hare Kan Kasar Yamen
Feb 11, 2017 02:49Shugaban Majalisar Kolin Gudanar da harkokin siyasa a kasar Yamen ya bukaci tsoma bakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan kawo karshen hare-haren wuce gona da iri da masarautar Saudiyya da kawayenta suke yi kan kasar Yamen.
-
Saudiya ta kori duban Ma'aikata yan kasar Pakistan
Feb 10, 2017 14:16Mahukuntan Saudiya sun kori duban Ma'aikata 'yan kasar Pakistan kan zarkin su nada alaka da hare-haren ta'addanci
-
Halba makami mai Lizzami zuwa yammacin birnin Riyad, ya razana masarautar Saudiya
Feb 10, 2017 10:21Makami mai Lizzami da Sojojin Yemen suka halba zuwa wani sansanin soja dake yankin Almazahimiya a yammacin birnin Riyad, ya razana magabatan Saudiya