-
Kwamitin Tsaron majalisar Dinkin Duniya Yana Yin Taron Sirri Akan Kasar Yemen
Jun 19, 2018 08:26Taron zai mai da hankali ne akan lalubo hanyoyin zaman lafiya da za a yi amfani da su domin warware rikicin kasar ta Yemen
-
Gwamnatin Iraqi Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Amurka Ta Kai Wa Dakarun Sa-Kai
Jun 19, 2018 08:23A ranar lahadin da ta gabata ne dai wani jirgin yakin Amurka ya harba makami mai linzami akan sansanin dakarun sa-kai na Hashdush-sha'abi wanda ya yi sanadin kashe mutane 22
-
Yunkurin MDD, Na Farfado Da Tattauwar Sulhu A Yemen
Jun 19, 2018 01:31Yunkurin na Majalisar Dinkin Duniya, na ganin ta farfado da tattaunawar sulhu tsakanin masu rikici a Yemen, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a birnin Hodaida wanda ya kunshi tashar ruwa a yammacin kasar ta Yemen.
-
Sojojin Yemen Sun Tabbatar Da Ci Gaba Da Rike Madafun Ikon Garin Hudaydah
Jun 19, 2018 01:21Mai magana da yawun sojojin kasar Yemen, Sharaf Luqman, ya bayyana cewar sojojin hadin gwiwan kasashen da suke yakar kasar Yemen karkashin jagorancin Saudiyya sun gaza wajen kwato sojojinsu da aka ritsa da su a garin Hudaydah duk kuwa da ci gaba da munanan hare-hren da suke ci gaba da kai wa gari ta sama.
-
Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kai Jerin Hare-Hare Kan Garin Hudaidah Na Yamen
Jun 18, 2018 14:45Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankunan garin Hudaidah na kasar Yamen.
-
Wani Matashin Palasdine Ya Yi Shahada A Gabashin Yankin Zirin Gaza Na Palasdinu
Jun 18, 2018 14:40Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wuta kan tawagar Palasdinawa a shiyar gabashin yankin Zirin Gaza lamarin da ya janyo shahadar bapalasdine guda.
-
Yemen: An Kashe Mayakan Da Saudiyya Take Goyawa Baya Masu Yawa A Hudaidah
Jun 18, 2018 07:35Majiyar tsaron kasar Yemen ta shaidawa tashar talabijin din al'alam cewa; Baya ga kashe daruruwan 'yan koren Saudiyyar, an kuma kona da lalata motocin yaki har 44
-
Palasdinu: Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama Ta Human Right Watch Ta Zargi HKI Da Laifukan Yaki.
Jun 18, 2018 07:32Kungiyar Kare hakkin bil'adaman ta Human Right Watch ta tabbatar da cewa haramtacciyar kasar Isra'ila ta tafka laifi akan mutanen Gaza kuma wajibi ne ga kungiyoyin kasa da kasa da su taka mata birki.
-
Ansarallah: Sojojin Makiya Suna Fuskantar Turjiya Mai Tsanani Wanda Basu Tsammani Ba A Bakin Ruwan Yammacin Kasar.
Jun 18, 2018 03:40Majiyar mayakan kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta bayyana cewa makiya a yakin da suke fafatawa yammacin kasar suna fuskantar tujiyan daga mutanen kasar wanda basu yi masa tanadi ba.
-
MDD Na Ci Gaba Da Tuntubar Masu Rikici A Yemen
Jun 17, 2018 13:31A daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a kusa da filin jirgin sama na Hodeida, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen, na ci gaba da tuntubar masu rikici akan samar da hanyoyin kauce wa jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali.