-
Dakarun Hashadu Sha'abi Sun Kai Hari Kan Ciboyoyin Da'esh A Siriya
Jun 14, 2018 01:19Dakarun sa kai na kasar Iraki dake yiwa lakabi da hashadu Sha'abi sun kai hari kan wasu wuraren mayakan kungiyar ISIS a kasar Siriya
-
MDD : Harin Da Saudiyya Ta Kaddamar A Hodeida Zai Kara Dagula Al'ammura A Yemen
Jun 13, 2018 10:16Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana ci gaba da tattaunawa domin kaucewa zubar da jini a birnin Hodeida na kasar Yemen, inda kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kaddamar da hari a yau Laraba.
-
UNICEF: Yara Miliyan 11 Ne Ke Bukatar Agaji A Kasar Yamen
Jun 13, 2018 08:02Asusu kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya sanar da cewa: Kananan yara miliyan 11 ne suke bukatar agajin gaggawa a Yamen sakamakon yakin da ke faruwa a kasar.
-
Dakarun Sa-Kai A Iraki Sun Dakile Hare-haren Da'esh A Yammacin Kasar
Jun 12, 2018 14:35A yau talata ne 'yan ta'addar kungiyar Da'esh da ke cikin kasar Syria su ka yi kokarin kutsawa cikin Iraki, sai dai dakarun sa-kai na Hashdu-Sha'aby sun yi nasarar dakile harin
-
Kira Kan Ci Gaba Da Aiwatar Da Kashe-Kashen Gilla Kan Palasdinawa
Jun 11, 2018 07:22Wani tsohon dan Majalisar Dokokin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya bukaci daukan matakin aiwatar da kashe-kashen gilla kan shugabannin kungiyar Palasdinawa ta Hamas.
-
Saudiyya : Wani Bafaranshe Ya Kashe Kansa Bayan Ya Fado Daga Saman Ka'aba
Jun 09, 2018 13:50Wani mutum dan asalin kasar Faransa ya kashe kansa ta hanyar fadowa daga kololuwar masallacin Ka'aba a Makkah.
-
Afganistan: Taliban Ta Amince Da Tsagaita Wuta Don Karshen Ramadan
Jun 09, 2018 10:09Kungiyar 'yan ta'adda ta taliban ta sanar da tsagaita buda wuta tsakaninta da sojojin Afganistan, a karshen watan Ramadan, wanda kuma shi ne irinsa na farko a cikin shekaru 17 bayan da sojojin kasashen ketare karkashin jagorancin Amurka suka kawar da mulkin daga hannun 'yan taliban din.
-
Akalla Palasdinawa 4 Ne Suka Yi Shahada A Zanga-Zangar Ranar Qudus Ta Duniya
Jun 09, 2018 02:06Harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan al'ummar Palasdinu da ke gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a jiya Juma'a a yankin Zirin Gaza, akalla Palasdinawa 4 ne suka yi shahada.
-
Jiragen Saman Yakin Saudiyya Suna Ci Gaba Da Yin Luguden Wuta Kan Kasar Yamen
Jun 07, 2018 13:37Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan yankunan lardin Hajjah da ke arewa maso yammacin kasar Yamen.
-
Mutane 16 Sun Mutu A Fashewar Rumbun Makamai A Iraki
Jun 07, 2018 01:16Rahotanni daga Iraki, na cewa mutane a kalla 16 ne suka rasa rayukansu, kana wasu kimanin talatin suka jikkata, biyo bayan fashewar wani rumbun makamai a Bagadaza babban birnin kasar.