UNESCO ta yi alawadai da kisan Dan jarida a kasar Brazil
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10198-unesco_ta_yi_alawadai_da_kisan_dan_jarida_a_kasar_brazil
UNESCO ta yi alawadai da kisan dan jaridar kasar Brazil sannan kuma ta bukaci magabatan da su gaggauta gudanar da bincike a kan lamarin.
(last modified 2018-08-22T06:58:49+00:00 )
Aug 27, 2016 01:03 UTC
  • UNESCO ta yi alawadai da kisan Dan jarida a kasar Brazil

UNESCO ta yi alawadai da kisan dan jaridar kasar Brazil sannan kuma ta bukaci magabatan da su gaggauta gudanar da bincike a kan lamarin.

Kamfanin dillancin Labaran Irna ne ya nakalto Irina Bokova Babbar Daraktar hukumar kare guraren tarihi na Duniya watau UNESCO na yin alawadai kan kisan gillar da aka yi wa wani dan jaridar kasar Brazil mai suna Miranda de Carmo kusa da gidansa a ranar Larabar da ta gabata.

A 'yan kwanakin nan an sha yiwa De Cormo barazana kafin daga bisani a hallaka shi, daga farkon wannan shekara zuwa yanzu wannan shi ne Dan jarida na 39  da aka kashe a kasar ta Brazil.

Har ila yau babbar Daraktar ta Hukumar UNESCO ta bukaci Gwamnatin ta Brazil da ta gaggauta gudanar da bincike domin zagulo wadanda suka aikata wannan aika aika tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

De Cormo shi ne shugaban Jaridar Sad Sam Sansura wacce ta yi kaurin suna wajen tsatsakar Gwamnati da 'yan siyasar kasar.