WHO Ta Ayyana Cutar Zika A Matsayin Babbar Barazana Ga Duniya
Feb 02, 2016 02:24 UTC
Kwararru na Hukumar sun bayyana cutar a matsayin wadda ke bukatar agajin gaggawa na Duniya.
Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana a wannan Litinin dokar ta baki akan cutar zika mai hadasa lahani ga jinjiri.
kwararu na hukumar ta WHO ko kuma OMS sun bayyana cutar a matsayin mai bukatar agajin gaggawa na kasa da kasa inji babbar darectar hukumar Margaret Chan.
Tuni dai kasar Brazil mai karbar bakucin gasar wasanin Olympique ta gargadi mata masu juna biyu da kada su halarci wasanin na bana.
Hukumar ta ce ana bukatar hada karfi da karfe tsakanin kasashen duniya domin magance yaduwar cutar da sauro ke hadaya, wace kawo yanzu ba tada magani ko riga kafi.
Tags