UNICEF: Yara miliyan 50 ke yin hijira a duniya
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF ya ce kusan yara miliyan 50 suke barin kasashensu na asli sanadiyar yake-yake, da kuma wasu matsalolin da kan tasowa cikin kasashen nasu
Asusun ya ce a shekara ta 2015 da ta wuce kimanin kishi 45 cikin dari na yaran 'yan gudun hijira da ke a karkashin kulawar MDD 'yan asilin kasashen Siriya ne da Afganistan wadanda yaki ya sa suka baro kasashensu.
Mataimakin daraktan asusun ya ce akwai bukatar a daina raba yara da iyayensu akasari 'yan ci rani masu neman mafaka.
A bangaren guda kuma, an bayyana cewa adadin 'yan gudun hijrar da ke zuwa kasar Jamus ya karu saosai.a shekarar 2015 din da ta gabata kimanin 'yan gudun hijra million guda ne suka shiga kasar ta Jamus.