Syria : An Dage Tattaunawa Tsakanin Kery Da Lavrov
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10741-syria_an_dage_tattaunawa_tsakanin_kery_da_lavrov
Jami'an diflomatsiya kasashen Amurka da Rasha sun sanar da cewa an dage tattaunawa kan batun Suriya ta tsakanin Sergueï Lavrov da John Kerry har zuwa ranakun takwas da tara na wanann wata.
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 07, 2016 12:38 UTC
  • Syria : An Dage Tattaunawa Tsakanin Kery Da Lavrov

Jami'an diflomatsiya kasashen Amurka da Rasha sun sanar da cewa an dage tattaunawa kan batun Suriya ta tsakanin Sergueï Lavrov da John Kerry har zuwa ranakun takwas da tara na wanann wata.

Majiyoyin diflomatsiyan kasashen biyu sun ce za'a ci gaba da tattauanwar ne a gobe Alhamis zuwa Juma'a a Geneva.

Hakan dai ya boyo bayan da sakataririn harkokin diflomatsiyan kasashen biyu suka tattauna ta wayar tarho yau Laraba akan yadda za'a cimma yerjejeniyar tsakanin AMurka da Rasha  akan yadda za'a yaki  gungun 'yan ta'ada da tura kayan agaji da kuma batun siyasa a kasar Siriya.

A kwana baya dai yumkurin fahimtar juna akan rikicin Siriya tsakanin Amurka da Rasha ya cutura bayan da kasashen suka watse ba tare da fahimtar juna ba akan sabanin dake tsakaninsu kan batun Syria.

Kasashen biyu dai sun  tattaunawa ne a daura da taron  kasashen G 20 mafiya yawan tattalin arziki a duniya daya gudana a kasar China.