Amurka Da Japon Na Son A Dauki Tsauraren Matakai Kan Pyongyang
Sep 11, 2016 10:45 UTC
Kasashen Amurka da Japon sun ce suna bukatar a dauki tsauraren matakai mafi dacewa akan shugaba Pyongyang na Koriay ta Arewa bayan gwajin makamin nukiliyar baya bayan nan.
Kasashen biyu sun ce suna aiki kafada da kafada da kwamitin tsaro na MDD akan matakan da zasu dauka na mayar da martani mai karfi ga Koriya ta Arewar
Ko baya ga hakan kasashen biyu tareda karea ta Kudu suna nazarin daukan wasu matakai makamatan wadannan ga Koriya ta Arewar saidai ba tare da yin karin haske ba.
A ranar Juma'a data gabata ce Koriya ta Arewa ta sanar da cewa tayi nasara gwada wani makamin nukiliya mafi girma duk da takunkuman da aka kakaba mata cen baya akan irin hakan.
Tags