David Camaroon ya yi murabus daga kujerar sa ta Majalisa
(last modified Tue, 13 Sep 2016 05:13:49 GMT )
Sep 13, 2016 05:13 UTC
  • David Camaroon ya yi murabus daga kujerar sa ta Majalisa

Watani biyu bayan yin murabus daga kujerar firaminista, Tsohon firaministan Burtaniya David Cameron ya sanar da yin murabus daga majalisar dokokin kasar.

Tashar Telbijin din Press Tv dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa a jiya Litinin  Tsohon Fira Ministan Birtaniya David Cameroon ya bayyana cewa babu wanda ya tilasta sa da yin murabus din.wannan mataki da Camaroo ya dauka zai wajabta gudanar da zabaen cike-gurbi a mazabarsa ta Witney dake Oxfordshire.Mista Camaron ya bayyana cewa zai yi iya kokarinsa wajen ganin kujerar da ya bari ba ta kubucewa Jam'iyarsa ta Conservative ba.

Bayan zaben raba-gardamar da aka gudanar a kan ci gaba da kasancewar Birtaniya a Tarayyar Turai a watan Yuni ne dai Mista Cameron ya yi murabus daga mukamin fira minista, sannan ya bayyana cewa  zai ci gaba da rike mukaminsa na dan majalisa har zuwa babban zabe na gaba.

Tun shekarar 2001 ne dai dan siyasar mai shekara 49 yake wakiltar mazabar Witney, a 2005 kuma ya zama jagoran jam'iyyar Conservative, sannan ya rike mukamin fira minista na tsawon shekara shida da 2010.