Jamus : An Cafke Siriyawa Uku Bisa Zargin Alaka da (IS)
Sep 13, 2016 06:41 UTC
Offishin mai gabatar da kara na gwamnatin Jamus a yau Talata ya sanar da cafke wasu 'yan gudun hijira uku 'yan asalin kasar Siriya bisa zarginsu da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta (IS).
Wata sanarwa da offishin ya fitar ta ce mutanen uku da suka shigo kasar ne a shekara data gabata a lokacin tururuwar 'yan gudun hijira Siriya dake neman mafaka a kasar.
Ana dai zargin mutanen ne da shigo kasar domin aiwatarda wasu umurni kungiyar ta (IS).
Sanarwar ta ce daya daga cikin mutanen da aka cafke mai suna Mahir Al-H, ya yi mubayi'a ga kungiyar ta IS a shekara 2015 kana ya samu wani gajeren horo na amfani da bindigogi a birnin Raqa dake zamen sansanin 'yan ta'addan a arewacin kasar Siriya.
Tags