Ban Ki-Moon Ya Jaddada Wajabci Kawo Karshen Rikicin Kasar Siriya
(last modified Tue, 20 Sep 2016 18:18:33 GMT )
Sep 20, 2016 18:18 UTC
  • Ban Ki-Moon Ya Jaddada Wajabci Kawo Karshen Rikicin Kasar Siriya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada wajabcin kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar Siriya.

A jawabinsa a bikin bude zaman babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 71 a yau Talata: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya jaddada wajabcin kawo karshen yakin basasar kasar Siriya.

Ban Ki-Moon ya fayyace cewa: Dukkanin masu karfi na kasashen duniya suna da hannu a yakin da ke ci gaba da aukuwa a kasar Siriya kuma suna da hannu dumu-dumu a zubar da jinin fararen hula.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan da wa'adin shugabancinsa ke daf da kawo karshe ya gabatar da shawarar samar da wata tawaga ta musamman da zata din ga tattauna matsalolin da suke addabar duniya da nufin samar da hanyar warware su.