Siriya / MDD : Akwai Wuya A Tattauna, Muddun Ana kai Farmaki
Sep 29, 2016 08:36 UTC
Wakilinn musamen na MDD, kan rikicin kasar Siriya, Staffan de Mistura, ya bayyana cewa akwai wuya a ci gaba da tattaunawa kan rikicin kasar Siriya mudun dai ana ci gaba da ruwan bama-bamai a ko ina.
Mr ya ce idan har za'a ci gaba da kai hare-hare ba kakkauatawa a wannan kasa, to yana da wahala sosai a ci gaba da tattaunawa domin samar da zamen lafiya a wannan kasa ta Siriya.
A ranar 22 ga watan nan ne Mista De Mistura ya bayyana fatansa na ganin anyi tattaunawar ta tsakanin masu rikici a kasar ta Siriya cikin makwani masu zuwa.
Sai dai kawo yanzu yanayin da ake ciki a kasar musamman yadda ake ta barin wuta da boma-bomai ya hana akai ko ina.
Tags