Wani Dan Kunan Bakin Wake Ya Halaka Kansa A Kasar Mali
Wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a kusa da sojojin kasar Sweden da suke aiki karkashin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali.
Majiyar Majalisar Dinkin Duniya a Mali ta sanar da cewa: Wani dan kunan bakin wake da ya yi jigida da bama-bamai ya tarwatsa kansa a kusa da tawagar sojojin kasar Sweden da suke gudanar da sintirin a wani yanki da ke kusa da garin Timbuktu a shiyar arewacin kasar Mali a yammacin jiya Litinin, inda nan take ya sheka lahira amma babu wani daga cikin sojojin na Sweden da ya samu koda rauni.
Kasar Sweden dai tana da sojojin 250 da suke aiki a karkashin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na {MINUSMA} da suke kasar Mali, kuma an tura sojojin ne tun a shekara ta 2013 bayan da kasar ta shiga cikin dambaruwar siyasa sakamakon juyin mulkin soji a shekara ta 2012 sannan gamayyar kungiyoyin 'yan ta'adda suka kwace iko da yankunan arewacin kasar ta Mali.