Za'ayi Taron Kasa da Kasa Kan Batun Syria A Wannan Asabar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12361-za'ayi_taron_kasa_da_kasa_kan_batun_syria_a_wannan_asabar
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar da cewa za'ayi wani taron kasa da kasa wanda zai hada dukkan masu ruwa da tsaki kan batun kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T06:59:04+00:00 )
Oct 12, 2016 12:07 UTC
  • Za'ayi Taron Kasa da Kasa Kan Batun Syria A Wannan Asabar

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar da cewa za'ayi wani taron kasa da kasa wanda zai hada dukkan masu ruwa da tsaki kan batun kasar Syria.

Za'a gudanar da taron ne a wannan Asabar a birnin Lausane na kasar Swizilend, inda ministocin harkokin wajen kasashe da dama ciki har da John Kery na Amurka da takwaransa Sergio Lavrov na Rasha, zasu tattauna hanyoyin shawo rikicin kasar Syria.

A wata hida da tashar talabijin ta CNN, ministan harkokin wajen Rasha ya bayyana cewa taron zai hada da Turkiyya, Saudiyya sai kuma killah kasar Qatar.

Wata majiya a gwamnatin Amurka ta tabbatar da haduwar, wace za ta kasance ta farko tun bayan cacar baki da aka fuskanta kwana baya tsakanin Amurka da Rasha kan batun kasar ta Syria, da ya kai ga ga dakatar da tattaunawar da suke kan batun tsagaita wuta a Syria. 

Alkaluma dai sun nuna cewa sama da mutane 300,000 ne suka rasa rayukansu a rikicin da aka shafe shekaru biyar anayi a wannan kasa ta Siriya.