An Zabi Antonio Guterres A Matsayin Sabon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12412-an_zabi_antonio_guterres_a_matsayin_sabon_sakataren_majalisar_dinkin_duniya
A kuri'ar da aka kada a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a yau din nan Alhamis, membobin Majalisar sun zabi tsohon firayi ministan kasar Portugal Antonio Guterres a matsayin sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan.
(last modified 2018-08-22T06:59:04+00:00 )
Oct 13, 2016 14:12 UTC
  • An Zabi Antonio Guterres A Matsayin Sabon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

A kuri'ar da aka kada a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a yau din nan Alhamis, membobin Majalisar sun zabi tsohon firayi ministan kasar Portugal Antonio Guterres a matsayin sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce a yau din nan Alhamis ne babban zauren ya zabi Antonio Guterres a matsayin sabon babban sakataren MDD wanda kuma shi ne zai zama babban sakataren majalisar na tara har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Mr.Antonio Guterres dan shekaru 67 a duniya zai maye gurbin babban sakataren majalisar na yanzu Ban Ki Moon dan shekaru 72 a duniya wanda zai sauka daga wannan mukamin a karshen wannan shekara ta  2016 bayan yayi wa'adi biyu na mulkinsa.

Mr Guterres ya rike mukamin firayi ministan Portugal din ne daga shekarar 1995 zuwa 2002 sannan kuma ya rike babban kwamishinan Majalisar Dinkin Duniyan kan lamurran 'yan gudun hijira daga shekara ta  2005 zuwa 2015.