Kisan da Aka yiwa Hariri akwai hannun Saudiya da HKI
Wani sanata na Amurka ya bayyana cewa HKI tare da taimakon masaurtar Ali sa'oud su ne suka kashe Rafic Hariri tsohon Piraministan kasar Labnon a shekarar 2005.
Tashar Telbijin din Rusiya Alyaum ta kasar Rasha ta nakalto sanatan Iowa State na kasar Amurka kalkashin Jam'iyar Repablicain Chuck Grassley na cewa sabin dalilan da muka samu na nuni da cewa Haramcecciyar kasar Isra'ila tare da taimakon kasar Saudiya ne suka kashe Rafic Hariri.
Mista Grassley shi ne shugaban Kwamitin shara'a na Majalisar Sanatocin Amurka a yayin hirar sa da Jaridar Paltico ya ce wasu dalilai da ingatattun shaidu sun nuna cewa Saudiya na da hanu kai tsaye a kisan gillar da aka yiwa Rafic hariri.
Wannan bayyani na zuwa ne yayin da dokar Janta ta samu amincewa a Majalisar Dokokin kasar Amurka wacce ta bayar da dama ga iyalan wadanda harin 11 ga watan Satumbar 2001 ya ritsa da su, shigar da karar Saudiya a kotuna daban daban na kasar,
Dan tsohon Piraminstan Sa'ad Hariri bisa goyon bayan Saudiya da Amurka sun yi ta kokarin daura wannan laifin kisa kan kungiyar Hizbul... inda suka yi amfani da kafafen yada labarai da dama da kuma bangarorin siyasa da Diplomasiya amma abin ya cutura.