Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya Ta Bukaci Tattaunawa Da Kasashen Afirka
(last modified Tue, 25 Oct 2016 12:42:12 GMT )
Oct 25, 2016 12:42 UTC
  • Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya Ta Bukaci Tattaunawa Da Kasashen Afirka

Kotun manyan laifuka ta duniya ta bukaci shiga tattaunawa da kasashen Afirka da suke da korafi kan ayyukanta, domin warware batun ta hanyar tattaunawa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Sidiki Kaba shugaban kwamitin alkalan babban kotun manyan laifuka ta duniya ne ya bayyana hakan, inda ya ce ficewar kasashen Afirka daga wannan kotu zai haifar da bababr illa ga kotun.

Tuna  cikin shekarar da ta gabata ce kasar Afirka ta kudu ta fara tattauna batun ficewarta daga kotun, bayan da ta fuskanci matsin lamba sakamakon rashin cafke shugaban Sudan Umar Hasan Albashir, inda majalisar dokokin kasar ta amince da hakan a cikin wannan wata na Oktoba.