Kwamitin tsaron MDD ya yi marhabin da zaben Michel Aoun
Kwamitin tsaron MDD ya yi marhabin da zaben Michel Aoun a matsayin sabon shugaban kasar Labanon.
Cikin wani Rahoto da suka watsa a jiya Talata manbobi 15 na kwamitin tsaron MDD sun ce kafa Gwamnatin hadin kai kasa da kuma gudanar da zaben 'yan Majalisa kafin watan Mayun 2017 shi zai karfafa zaman lafiyar kasar Labanon da kuma tunkarar duk wata barazana da yankin ke fuskanta.
Sanarwar ta bukaci dukkanin bangarorin siyasar kasar da su yi azama wajen magance matsalar da kasar su ke fuskanta tare kuma hada kan 'yan kasar, har ila yau sanarwar ta kara da cewa kiyaye zaman lafiyar Labanon na a matsayin zaman lafiya da tsaron yankin ne.
Zaben Michel Aoun a matsayin shugaban kasar Labanon na a matsayin wani mataki mai mahimanci na magance rikicin siyasar kasar da kungiyoyin kasa da kasa suka jima cikin jira.
A ranar Litinin din da ta gabata ne 'yan Majalisar Dokokin kasar Labanon suka zabi Michel Aoun a matsayin sabon shugaban kasar bayan da kasar ta kwashe shekaru biyu da rabi ba tare da Shugaban kasa ba.