Kungiyar Tsaro Ta NATO Na Shirin Shiga Tattaunawa Da Rasha
Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO ya bayyana cewa suna kokarin ganin sun koma kan teburin tattaunawa tare da kasar, domin rage sabanin da ke tsakaninsu.
Kamfanin dillanicn labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya fadi a zaman ministocin tsaro na kasashen kungiyar a birnin Brussels na kasar Belgium, cewa sun cimma matsaya kan wajabcin shiga tattaunawa da Rasha domin rage zaman doya da manja da a ke yi a tsakaninsu da ita.
Ya kara da cewa Rasha ita ce kasa mafi girma da take makwaftaka da nahiyar turai,a kan haka dole ne a warware matsalolin da ke tsakani ta hanyar tattaunawa, ba sai ta hanyar tayar da jijiyoyin wuya ba.
Dangane da fargaban da wasu kasashen kungiyar ke yi na yiwuwar ficewar Amurka daga kungiyar, Jens Stoltenberg ya bayyana cewa zaben Trump ba zai sanya Amurka ficewa daga kungiyar ba.