An Kammala Taro Kan Dumamar Yanayi A Morocco
Jiya Alhamis an kammala taro kan dumamar yanayi daya gudana a kasar marocco inda aka amince da wani kuduri dake kira ga daukacin masu ruwa da tsaki da su dora matukar muhimmanci tare da hadin gwiwa wajen yaki da tasirin sauyin yanayi.
Babban kalubalen da ke gaban wakilan kasashe 196 a taron sauyin yanayin, shi ne yadda za su aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a birnin Paris na Faransa kan rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli a duniya.
Saidai ana tunanin lamarin zai iya daukar sabon salo sakamakon nasarar da dan takarar jamiyyar Republican Donald Trump ya samu a zaben shugabancin Amurka.
Dama dai tun a lokacin yakin neman zabensa, mista Trump, ya bayyana batun na sauyin yanayi da cewa tamkar "wasan yara ne" kuma ya lashi takobi soke duk wasu kudurori da gwamnatin Obama ta dauka, musamman game da rattaba hannun da Amurkar ta yi kan yarjejeniyar Paris.
Amurka dai na cikin kasashen duniya da suka sa hannu a yarjejeniyar kuma masana na ganin yana da wahala a cimma biyan bukata ba tare da Amurka ba.