An kashe wani babban jami'in tsaro a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i14362-an_kashe_wani_babban_jami'in_tsaro_a_somaliya
Wani babban jami'in tsaron Somaliya ya rasa ransa yayin da wasu uku na daban suka jikkata sanadiyar wani harin Bam a birnin Magadushu
(last modified 2018-08-22T11:29:17+00:00 )
Nov 25, 2016 05:52 UTC
  • An kashe wani babban jami'in tsaro a Somaliya

Wani babban jami'in tsaron Somaliya ya rasa ransa yayin da wasu uku na daban suka jikkata sanadiyar wani harin Bam a birnin Magadushu

kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto Abdifitah Omar Halane kakakin Magajin garin birnin Magadushu na cewa a marecen jiya Alkhamis wata Mota da aka danawa Bam ta tashi a wata babbar hanya mai yawan tsunkoson Al'umma dake yankin Shibis na birnin Magadushu, harin da ya yi sandiyar mutuwar wani babban jami'in tsaron kasar tare da jikkata wasu uku na daban.

Kakakin Magajin garin Magadushun ya tabbatar da cewa jami'an 'yan sanda sun fara gudanar da bincike kan harin tare kuma da kokarin zagulo wadanda suka kai shi.ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

Wannan hari dai na zuwa ne a yayin da Jami'an tsaron Somaliyan tare da hadin gwiwar Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka AMISON suka ce sun karfafa matakan tsaro a fadin kasar gaba daya domin a samu a gudanar da zaben Shugaban kasar da za a yi ranar 30 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki cikin tsaro.