Sabon Babban Sakataren MDD Yayi Rantsuwar Kama Aiki
Tsohon Firayi ministan kasar Portugal Antonio Guterres, yayin rantsuwar kama aiki a matsayin sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na tara wanda zai kama aiki a watan Janairun shekara mai kamawa ta 2017.
Rahotanni daga birnin New York helkwatar Majalisar Dinkin Duniyan sun bayyana cewar shugaban babban zauren MDDn Peter Thomas ne ya rantsar da Mr. Guterres a gaban membobi 15 na kwamitin tsaron MDD da sauran membobin majalisar don kama aiki a matsayin sabon babban sakataren majalisar bayan da wa'adin babban sakataren na yanzu Ban Ki Moon zai kare a karshen shekarar nan.
A jawabin da yayi bayan rantsuwar kama aikin, Mr Guterres ya ce wajibi ne a yi gyare-gyare wa tsarin gudanarwar Majalisar don cimma manufar da ake son cimmawa, kamar yadda ya ce akwai bukatar a saurari korafe-korafen da sauran membobin majalisar suke da su don a kara tabbatar da hadin kan majalisar.
Mr. Guterres, dan shekaru 67 a duniya, ya rike matsayin firayi ministan kasar Portugal daga 1995 to 2002, kamar yadda kuma ya rike matsayin babban kwamitin MDD kan lamurran 'yan gudun hijira daga shekarun 2005 zuwa 2015. An zabe shi ne a matsayin babban sakataren MDD a ranar 13 ga watan Oktoban wannan shekara ta 2016.