Ronaldo Ya Lashe Kyautar Ballan d'Or Ta Shekarar 2016
Sanannen dan kwallon kafan kungiyar nan ta Real Madrid ta kasar Spain, Cristiano Ronaldo, ya lashe kyautar dan kwallon kafa na duniya da ya fi yin fice a shekara ta 2016 da aka fi sani da kyautar Ballon d'Or.
Wannan dai shi ne karo na hudu da Cristiano Ronaldo, dan shekaru 31 wanda kuma dan kasar Portugal ne yake lashe wannan kyauta, bayan da 'yan jaridu daga sassan duniya 173 suka jefa masa kuri’a sama da babban abokin hamayyarsa Lionel Messi dan kasar Argentina wanda kuma yake bugawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
A kakar wasan ta bana, Ronaldo ya samu nasarar jefa kwallaye 48 a wasanni 52 da ya bugawa kungiyarsa ta Real Madrid da kuma kasarsa ta Portugal, kamar yadda ya taimakawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid din lashe kofin zakaraun Turai da kuma kasar Portugal cin kofin nahiyar Turai a 2016.
Wannan dai shi ne karo na hudu da Ronaldo ya ke lashe wannan kyautar ta Ballon d'Or wato a shekarun 2008 da 2013 da kuma 2014 sai kuma na bana 2016. Har ya zuwa yanzu dai Lionel Messi ne ke kan gaba, wanda ya lashe kyautar har sau biyar.