Kwararrun Kasar Rasha Sun Fara Biciken Kashe Jakadar Kasar A Turkiya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i15514-kwararrun_kasar_rasha_sun_fara_biciken_kashe_jakadar_kasar_a_turkiya
Kwana guda bayan kisan gillan da aka yi wa jakadar kasar Rasha a Ankara na kasar Turkiyya, wata tawagar kwararru masu bincike na kasar Rasha sun isa kasar Turkiyan da nufin gano yadda aka kashe jakadan.
(last modified 2018-08-22T11:29:25+00:00 )
Dec 20, 2016 18:20 UTC
  • Kwararrun Kasar Rasha Sun Fara Biciken Kashe Jakadar Kasar A Turkiya

Kwana guda bayan kisan gillan da aka yi wa jakadar kasar Rasha a Ankara na kasar Turkiyya, wata tawagar kwararru masu bincike na kasar Rasha sun isa kasar Turkiyan da nufin gano yadda aka kashe jakadan.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya jiyo ministan harkokin wajen kasar Rashan Sergei Lavrov a jawabin da yayi wajen taron kasashe uku tsakanin Iran, Rasha da Turkiyya kan rikicin kasar Siriya yana cewa tuni kwararru masu bincike daga Rashan suka isa kasar Turkiyyan don gudanar da bincike kan yadda aka kashe jakada Andrei Karlov.

Mr. Lavrov ya ce tuni shugabannin Rasha Vladimir Putin da na Turkiyyan Rajab Tayyib Erdogan, cikin wata tattaunawa da suka yi suka cimma matsayar gudanar da bincike kan wannan lamari tare da taimakon kwararrun kasar Rashan.

A jiya ne dai wani tsohon dan sandan kasar Turkiyyan ya harbe jakadan Rashan a birnin Ankara na kasar Turkiyya  yayin da yake jawabi a wani wajen taron baje koli lokacin da maharin ya fara harbe-harbe yana ta kabbara tare da cewa kada a manta da Aleppo kada a manta da Syria.