Gwmnatin Myanmar Na Shirin Raba Musulmi Da Yankunansu
(last modified Tue, 27 Dec 2016 17:36:39 GMT )
Dec 27, 2016 17:36 UTC
  • Gwmnatin Myanmar Na Shirin Raba Musulmi Da Yankunansu

Gwamnatin kasar Myanmar na shirin raba wasu musulmi da yankunansu, tare da zaunar da wasu 'yan addinin Buda a cikin yankunan nasu a garin Mangdo da cikin lardin Rakhin.

Kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, mahukunta a lardin Rakhin na kasar Myanmar, sun gina wasu kauyuka guda bakwai a wasu yankuna da ke cikin lardin na Rakhin, da nufin zaunar da musulmi da suke a garin Mangdo.

Mahukuntan suka ce asalin garin Mangdo na mabiya addinin Buda ne, amma daga bisani 'yan kabilar Rohingya da suka shigo cikin kasar daga Bangadasha suka zauna wurin, a kan haka mabiya addinin Buda za su dawo wurinsu, yayin da muuslmin da ke wurin za a mayar da su zuwa kauyukan da aka gina musua  wasu wuraren na daban.

Fiye da kashi 98 na mutanen da suke zaune a wannan gari dai mabiya addinin muslunci ne 'yan kabilar Rohingya, yayin da adadin masu bin addinin Buda a garin bai wuce kashi 2 cikin dari ba, kuma muuslmi suna zaune da su lafiya tsawon daruruwan shekaru ba a taba jin tsakaninsu.

Kimanin watanni da suka gabata ne dai jami'an tsaron gwamnatin Myanmar suka yi wa musulmi kisan gilla a wannan yanki, tare da kone musu gidaje da kaddarori.