Korea Ta Arewa Ta Harba Makamai A cikin Ruwa.
(last modified Thu, 03 Mar 2016 07:29:23 GMT )
Mar 03, 2016 07:29 UTC
  • Korea Ta Arewa Ta Harba Makamai A cikin Ruwa.

Kasar Korea Ta Sake Harba Wasu Makamai A cikin Ruwa.

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya nakalto cewa; Da Safiyar yau alhamis kasar Korea ta Arewa ta harba wasu makami a cikin ruwa.

Harba makamai na yau da Korea ta yi ya zo ne jim kadan da kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya ya amince da kakabawa kasar wasu sabbin takunkumai saboda gwajin makami mai linzami masu cin dogon zango da ta yi a makwannin da su ka gabata.

Ministan tsaron kasar Korea ta Kudu Mon Sang ya fadawa manema labaru cewa; Da misalin karfe 10 na safiyar yau ne Korea ta Arewan ta harba makaman masu linzami da ke cin gajeren zango a cikin tekun gabas, wanda ake kira da tekun Japan."

Ministan tsaron kasar ta Korewa ta kudu ya ci gaba da cewa; kasarsa tana ci gaba da sanya idanu akan abinda Korea ta Arewa za ta iya aikatawa anan gaba."

Harba takunkumin da Korea ta Arewan ta yi dai ya zo ne bayan wasu sa'aoi da majalisar dinkin duniya ta amince da kakabwa kasar takunkumi.