MDD Ta Goyi Bayan Shirin Tsagaita Wuta A Siriya
Majalisar dinkin duniya ta goyi bayan shirin tsagaita wutar da kasashen Rasha da Turkiyya suka samar a Syria.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da rahotanni ke cewa an samu dan sukuni a cikin kwananki biyu na tsagaita wutar, koda yake dai an samu karya yarjejeniyar a wasu wurare da kuma harin da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai.
A zamensa na jiya Asabar kwamitin tsaro na MDD ya amince da gagarimin rinjaye da shirin tsagaita wutar da ya fara aiki da yammacin ranar Alhamis data gabata.
MDD dai na fatan wannan shirin da kasashen Rasha da Turkiya suka cimma, zai taimaka wajen samar da tattaunawar zamen lafiya tsakanin gwamnatin Syria da 'yan adawa domin kawo karshen yakin da aka shafe kusan shekaru shida ana yi a wannan kasa ta Syria.
A ranar 29 ga watan Disamba da mukayi ban kwana dashi ne kasashen Rasha da Turkiyya suka cimma shirin tsagaita wuta a Syria, saidai shirin baiu shafi yakin da akeyi da 'yan ta'addan IS ba.