Shugaba Hollande Zai Ziyarci Iraki
Jan 01, 2017 06:22 UTC
Shugaba François Hollande na Faransa ya sanar da cewa zai isa kasar Iraki a wannan Litinin, domin jinjinawa sojojin kasarsa dake fagen daga a yaki da ta'addanci a kasar ta Iraki.
Mista Hollande ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa na sabuwar shekara nan ta 2017 da muka shiga, inda ya kara da cewa bamu kai ga kawo karshen ta'addanci ba, don haka zamu ci gaba da yakarsa.
Wannan shi ne ma manufar jibge dakarunmu a kasashen Mali, Syria da Iraki inda zani kai ziyara ranmar Litinin domin jinjinawa sojojin mu, inji Mista Hollande.
Ko a watan Satumban shekara 2014, Shugaba Hollande ya ziyarci kasar ta Iraki inda yayi alkawarin taimakawa kasar da sojoji wajen yaki da 'yan ta'addan IS.
Tags