MDD : Guterres, Zai Gabatar Da Jadawalin Mayan Ayyukansa Ga Kwamitin Tsaro
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16348-mdd_guterres_zai_gabatar_da_jadawalin_mayan_ayyukansa_ga_kwamitin_tsaro
Sabon sakatare janar na MDD, Antonio Guterres zai gabatar da jawabinsa na farko yau Talata gaban kwamitin na MMD inda zai bayyana manyan ayyukan da zai sa a gaba.
(last modified 2018-08-22T06:59:30+00:00 )
Jan 10, 2017 03:05 UTC
  • MDD : Guterres, Zai Gabatar Da Jadawalin Mayan Ayyukansa Ga Kwamitin Tsaro

Sabon sakatare janar na MDD, Antonio Guterres zai gabatar da jawabinsa na farko yau Talata gaban kwamitin na MMD inda zai bayyana manyan ayyukan da zai sa a gaba.

Tsohon firaministan Portigal, Mista Guterres wanda ya gaji Ban Ki Moon a ranar daya ga watan Janairun nan, ya nakalto kadan daga cikin muhimman ayyukan da zai maida hankali akansu, wadanda suka hada da rikicin kasar Syria da kuma zubar da jini a Sudan ta Kudu.

Mista Guterre, wanda yayi alkawarin maido da martabar kungiyar nada babban kalubale a gaban kwamitin tsaro na MDD wanda ke fuskantar rarrabuwar kawuna musammen kan yakin da ake shafe shekaru shida ana  yi a kasar Syria.

Kafin hakan dai sabon sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, ya bayyana a wata muhawara cewa babbar kasawa ita ce yadda yau kasahen duniya suka kasa wajen hana rikice rikice da kuma tabbatar da zamen lafiya a doron duniya nan.

Ya kara da cewa dole ne a inda akwai rikici ko yaki ko fahimtar juna, mu zama masu shiga tsakani, da kuma tabbatar da diflomatsiya wace dukkan kasashe masu sabani zasu amunce da ita.