Venezuela : An Kama Dan Majalisa Da Bindiga Da Abubuwa Masu Fashewa
(last modified Thu, 12 Jan 2017 16:55:24 GMT )
Jan 12, 2017 16:55 UTC
  • Venezuela : An Kama Dan Majalisa Da Bindiga Da Abubuwa Masu Fashewa

Rahotanni daga Venezuela na cewa an kama wani dan majalisa na bangaren adawa da bindiga da harsashai da kum abubuwa masu fashewa.

Wani jami'in rundinar musamen da shugaban kasar Nicolas Maduro ya kasa domin kalubalantar duk wani shiri na juyin mulki ne ya cafke dan majalisan mai suna Gilber Caro.

Sabon mataimakin shugaban kasar ne Tareck El Aissami ya bayyana cewa an cafke dan majalisan da bindiga kira mai sarafa kanta da kuma caja-caja na harsashai har guda 20 da kuma wasu abubuwa masu fashewa uku kirar C-4.

An dai ce dan majalisan da kuma wasu mutane na kokarin tada hankali ne a kasar.

Saidai shugaban majalisar dokokin wanda na bangaren adawa ne ya yi tur da kamun dan majalisa tare da kiar da'a mutunta dan majalisa saboda rigar kariya da yake da ita.