Amurka Ta Kakabawa Wasu Mayan Jami'an Syria Takunkumi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16522-amurka_ta_kakabawa_wasu_mayan_jami'an_syria_takunkumi
Karon farko, Amurka ta kakabawa wasu mayan jami'an gwamnatin Syria su 18 takunkumi saboda zargin da akeyi wa sojojin Syria na amfani da makamai masu guba.
(last modified 2018-08-22T06:59:32+00:00 )
Jan 12, 2017 13:52 UTC
  • Amurka Ta Kakabawa Wasu Mayan Jami'an Syria Takunkumi

Karon farko, Amurka ta kakabawa wasu mayan jami'an gwamnatin Syria su 18 takunkumi saboda zargin da akeyi wa sojojin Syria na amfani da makamai masu guba.

Wata sanarwa da fadar Wite House ta fitar a yau ta amfani da makami mai guba kan al'umma abun allawadai ne kuma ya sabawa yarjejeniyar duniya na kerawa da kuma amfani da makamai masu guba.

koda yake dai labarin bai ambato sunayen mutanen da takunkumin ya hau akan su, aman ya ce akwai mayan jami'an tsaro da kuma wasu jagororin wata cibiyar bincike.

Hukumomin AMurkar dai sun yi amfani ne da rahoton da MDD ta fitar a watan Oktoba bara wanda ya zargi dakarun Syria da kai hari da makamai masu guba a biranen Tell Mannas Qmenas da Sarmin, a lardin Idleb, dake arewa maso yammacin kasar ta  Syria.

Takunkumin dai ya shafi toshe kaddarori ko dukiyar jami'an da kuma hana su shiga Amurkar.

Amurka ta kuma yi amfani da wannan damar inda tayi kira ga dukkan kasashe memba a MDD da kuma wadanda suka sanya hannu a yarjejeniyar amfani da makamai masu guba dama Rasha dasu dauki mataki irin wannan.

Sau tarin yawa dai AMurka da kawayen ta na zargin hukumomin  Syria da yin amfani da makamai masu guba, alhali so tarin yawa akan gano ire iren wadanan muggan makamai ga 'yan tawaye da Amurkar ke marawa baya.