Rasha Ta Gayyaci Bangaren Trump A Tattaunawar Syria
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16570-rasha_ta_gayyaci_bangaren_trump_a_tattaunawar_syria
Kasar Rasha ta juyawa gwamnatin Obama baya, inda ta gayyaci bangaren zababen shugaban kasar Donald Trump a tattaunawar neman sulhu kan rikicin kasar Syria .
(last modified 2018-08-22T06:59:32+00:00 )
Jan 14, 2017 02:53 UTC
  • Rasha Ta Gayyaci Bangaren Trump A Tattaunawar Syria

Kasar Rasha ta juyawa gwamnatin Obama baya, inda ta gayyaci bangaren zababen shugaban kasar Donald Trump a tattaunawar neman sulhu kan rikicin kasar Syria .

Jaridar Washington Post, ta ce gwamnatin shugaban kasar mai barin gado Barack Obama ta ce har kayo yanzu bata samu wata gayyata ba a hukumance daga Rasha na shiga tattaunawar da za'ayi a ranar 23 ga watan nan a birnin Astan na kasar Kazakhstan.

Kafin hakan dai gwamnatin Obama ta shawarci bangaren zababen shugaban kasar da ya shiga tattaunawar da kasashen Rasha, Iran da Turkiyya suka shiya.

Tattaunawar da za'ayi a Birnin Astana zata zo ne daidai lokacin da sabuwar gwamnatin Trump zata fara aiki.

A watan Disamba na shekara data gabata ne kasashen Rasha, Iran da Turkiyya suka sanar da yin tattaunawar ta masu ruwa da tsaki kan makomar Syria bayan cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kuma wannan shi ne karon farko da aka shirya wata tattaunawa kan makomar Syria ba tare da Amurka ba, wacce aka sani cewa ita ta jagoranci kusan dukkan tattaunawar da aka yi kan rikicin kasar ta Syria a shekarun baya baya nan.