Sabon Sakataren MDD Ya Bayyana Shekarar 2017 A Matsayin Shekarar Sulhu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16801-sabon_sakataren_mdd_ya_bayyana_shekarar_2017_a_matsayin_shekarar_sulhu
Sabon babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana shekara ta 2017 a matsayin shekara ta zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummomin duniya.
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 19, 2017 03:20 UTC
  • Sabon Sakataren MDD Ya Bayyana Shekarar 2017 A Matsayin Shekarar Sulhu

Sabon babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana shekara ta 2017 a matsayin shekara ta zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummomin duniya.

Antonio Guterres ya bayyana hakan ne a wani taro da aka shirya a birnin New York na kasar Amurka domin nuna adawa da kyamar da ake nuna wa musulmi a Amurka da ma wasu kasashen duniya.

Ya ce ko shakka babu akwai abubuwa da suke faruwa da ba su da dadin ji, na kyma da ake nuna wa wasu a duniya, ko dai saboda addininsu ko launin fatarsu ko abin da ya yi kama haka, har ma da cin zarafinsu, kuma akwai irin wadannan abubuwa da suka faru a wasu wuraren wadanda ba ji labari ba.

Sabon babban sakataren majalisar dinkin duniya ya ce zai iyakacin kokarinsa domin ganin an takawa cin zarafin dan adam birki a duniya, tare da kare hakkokinsa da akidarsa da mutuncinsa, da rayuwarsa da karamarsa.