An Fara Taron Tattaunawar Sulhun Kasar Siriya A Kasar Kazakhstan
A yau ne aka faraa wani taron tattaunawar sulhu tsakanin wakilan gwamnati da 'yan adawan kasar Siriya a birnin Astana babban birnin kasar Kazakhstan da nufin samo hanyar da za a magance rikicin kasar da ya ki ci ya ki cinyewa.
Rahotanni sun ce ministan harkokin wajen kasar Kazakhstan din Kairat Abdrakhmanov shi ne ya bude taron na kwanaki biyu karkashin sanya ido da kuma shiga tsakanin kasashen Iran, Rasha, da Turkiyya bugu da kari goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.
Wadannan kasashe ukun dai, wato Iran, Rasha da Turkiyya su ne suka shirya taron bayan amincewar gwamnatin Siriya da 'yan tawayen kasar inda gwamnatocin kasashen Iran da Rasha za su zamanto masu shiga tsakanin ta bangaren gwamnatin Siriya, alhali ita kuma kasar Turkiyya wacce ta jima tana goyon bayan 'yan adawan Siriyan za ta kasance mai shiga tsakani a madadinsu.
Taron wanda za a gudanar da shi a asirce ana sa ran zai samar da hanyar da za a magance rikicin kasar Siriya da ya dauki shekaru shida ana yi.