Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Na Musamman Ya Isa Kasar Gambiya
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya aike da wakilinsa na musamman zuwa kasar Gambiya domin zantawa da mahukuntan kasar bayan samun canjin gwamnati a kasar ta Gambiya.
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric a jiya Alhamis ya sanar da cewa: Muhammad Ibnu Chambas wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kasar Gambiya ya isa birnin Banjul fadar mulkin Gambiya, inda zai tattauna da sabon shugaban kasar Adama Barrow da wakilan jam'iyyun siysar kasar gami da kungiyoyin fararen hula.
Stephane Dujarric ya kara da cewa: Daga cikin manyan ayyukan Muhammad Ibnu Chambas har da tattauna batun hanyoyin mika ragamar shugabancin kasar Gambiya ga sabon zababben shugaba kasar Adama Barrow.