Jami'an Tsaron Myanmar Suna Ci Gaba Da Muzgunawa Musulmi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17169-jami'an_tsaron_myanmar_suna_ci_gaba_da_muzgunawa_musulmi
Jami'an Tsaron kasar Myanmar sun kame musulmi 23 bisa tuhumar cewa sun buga wa wasu danginsu waya da suke zaune a wajen kasar.
(last modified 2018-08-22T11:29:36+00:00 )
Jan 30, 2017 12:44 UTC
  • Jami'an Tsaron Myanmar Suna Ci Gaba Da Muzgunawa Musulmi

Jami'an Tsaron kasar Myanmar sun kame musulmi 23 bisa tuhumar cewa sun buga wa wasu danginsu waya da suke zaune a wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron kasar ta Myanmar sun kame musulmi ne 'yan kabilar Rohingya su 23, wadanda suka tafi da wani wurin da ba a sani ba, inda suka bayar da hujjar cewa mutanen sun buga waya ne zuwa ga danginsu da suke zaune a wajen kasar.

Baya ga hakan kuma jami'an tsaron sun ce mutanen sun zauna a cikin masallaci fiye da mintuna goma bayan sallar Magariba, duk kuwa da cewa an kafa doka a kan musulmi kan su gaggauta ficewa daga cikin masallaci da zaran sun kammala sallar magariba, tare da hana su gudanar da sallar isha'i a cikin masallatai.

Makonni biyu da suka gabata ne ministocin harkokin wajen kasashen musulmi suka gudanar da zama a birnin Kualalampour na kasar Malayzia, inda suka tattauna kan halin da musulmin kasar Maynmar ke ciki, da kuma taimakon da za su iya ba su.