Rasha ta karyata labarin mutuwar Sojojin ta a Siriya
Kakakin Ma'aikatar tsaron Rasha ya karyata rahoton da aka watsa na mutuwar Sojojin kasar A Siriya
A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Lahadi, Kakakin Ma'aikatar tsaron Rasha Igor Konashenkov ya ce Rahoton da tashar Telbijin din Aljazira ta kasar Qatar ta watsa dangane da mutuwar Sojojin kasar Rasha biyar a kasar Siriya sanadiyar Bam da ya tashi da wata Motar Soja a gefen garin Lazikiya karya ce.
Mai magana da yawun Ma'aikatar tsaron ta Rasha ya kara da cewa dukkanin Sojojin kasar dake aiki a kasar Siriya suna cikin koshin Lafiya, kuma irin wadannan karyace karyace ba zai hanasu ci gaba da aiyukan su a kasar ta Siriya ba.
A daren jiya Assabar ne, tashar telbijin din Aljazira ta sanar da cewa Sojojin Rasha biya sun hallaka sanadiyar Bam da ya tashi da wata Motar Soja a gefen garin Lazikiya.