Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren Birnin Bagadaza
Babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da hare-haren bama-baman da aka kai a birnin Bagadaza na kasar Iraki wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 60.
A cikin wani bayani da ya fitar a jiya, babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya bayyana hare-haren da aka kai a yammacin ranar Alhamis da ta gabata a birnin Bagadaza na Iraki da cewa aiki na dabbanci.
Ya ce majalisa dinkin duniya za ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Iraki domin yaki da ayyukan ta'addanci a cikin kasar gadan-gadan.
Kungiyar ISIS wadda kasashen turai da na wasu larabawa suka kafa, ta dauki alhakin kai harin, inda ta tayar da bama-bamai a yankin Biya'a da ke kudancin birnin bagadaza, inda a nan take mutane 55 suka rasa rayukansu, daga bisani kuma adadin ya ci gaba da karuwa.