Rasha ta aike da taimakon agaji zuwa Siriya
Kakakin cibiyar sa ido kan tsagaita wuta a kasar Siriya ta kasar Rasha ya bayyana cewa Dakarun tsaron cibiyar sun kai sama da tom miliyar guda da rabi na gayan abinci zuwa garin Al-Skelbia na jihar Hummah dake cikin kasar Siriya
Cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Litinin Kakakin Cibiyar dake sa ido a tsagaita wuta na kasar Siriya Mista Alexei ya bayyana cewa Cibiyar ta aike da Tom sama da miliyan daya da rabi na kayan abinci da magani zuwa ga mazauna garin Al-Skelbia na kasar Siriya da adadinsu ya kai dubu 20
Mista Alexei ya kara da cewa taimakon ya hada shinkafa, garin fulawa, suga gami da abincin kwankwani, kuma tuni aka raba su tsakanin Al'ummar wannan gari.
Har ila yau cibiyar ta kafa asibicin ficin gadi tare kuma kwararrun likitoci na Rasha domin kula da marassa lafiya na wannan gari.
A Bangare guda mazauna garin na Al-Skelbia sun sanar da cewa a 'yan kwanakin da suka gabata 'yan ta'adda sun halba rokoki a cikin garin, sama da Dakarun sa kai na wannan gari 700 ne sun sunturi domin kare garin su daga hare-haren 'yan ta'adda.