Wakilin Rasha A MDD, Vitaly Churkin, Ya Rasu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17856-wakilin_rasha_a_mdd_vitaly_churkin_ya_rasu
An yi shiru na minti daya domin nuna juyayi kan rasuwar wakilin Rasha a MDD Vitaly Churkin, kafin kuma a gudanar da cikakken zaman taron MDD karo na 71.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 21, 2017 02:23 UTC
  • Wakilin Rasha A MDD, Vitaly Churkin, Ya Rasu

An yi shiru na minti daya domin nuna juyayi kan rasuwar wakilin Rasha a MDD Vitaly Churkin, kafin kuma a gudanar da cikakken zaman taron MDD karo na 71.

A jiya ne wakilin na Rasha a MDD, Mr Churkin, ya rasu a hedkwatar MDD dake birnin New York. 

Rahotanni sun bayyana cewa a jiya Litinin, zaunanniyar tawagar wakilan kasar Rasha dake MDD ta shaida cewa Mr. Churkin ya rasu ne a yayin da yake aiki a ofishinsa,a daidai lokacin da ake shirin taya shi murnar cika shekaru 65 a yau Talata.

Wasu majioyoyin diflomatsiyya sun ce Mirigayin ya mutu ne saboda matsalar zuciya.

Shugaban babban taron MDD karo na 71 Peter Thomsen, ya ce ya kadu matuka da gaske game da rasuwar Mr. Churkin.