Jami'an Diflomasiyyar Turkiya 136 Sun Nemi Mafakar Siyasa A Jamus
(last modified Sun, 26 Feb 2017 06:44:50 GMT )
Feb 26, 2017 06:44 UTC
  • Jami'an Diflomasiyyar Turkiya 136 Sun Nemi Mafakar Siyasa A Jamus

Jami'an diflomasiyyar kasar Trkiya 136 ne suka nemi mafakar siyasa daga gwamnatin kasar Jamus, wadanda dukkaninsu suna dauke ne da fasfo na diflomasiyya.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya bayar da rahoton cewa, a bisa rahoton da ma'aikatar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Jamus ta fitar, ta tabbatar da cewa daga lokacin da aka yi yunkurin juyin mulki a kasar Turkiya a cikin watan Agustan 2016, ya zuwa farkon watan Janairun 2017, jami'an diflomasiyyar kasar Turkiya 136 suka mika bukatarsu ga gwamnatin Jamus, kan a ba su mafaka ta siyasa.

Tun bayan yunkurin juyin mulkin wanda bai yi nasara ba, gwamnatin Erdogan ta kame dubban sojoji da kuma dubban 'yan sanda, gami da daruruwan alkalai da 'yan jarida da ma 'yan siyasa, duk bisa zarginsu da goyon bayan Fathullah Golen, wanda gwamnatin Turkiya ke zarginsa da hannu wajen shirya juyin mulkin.

Kungiyar tarayyar turai ta zargi Erdogan da yin amfani da wannan damar domin muzgunawa duk wani wanda yake adawa da salon mulkinsa a kasar.