Wakilan MDD Na Ziyara A Yankin Tafkin Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18162-wakilan_mdd_na_ziyara_a_yankin_tafkin_chadi
Wata tawagar wakilan kwamitin sulhu na MDD na shirin soma wata ziyara yau Alhamis a yankin tafkin Chadi domin janyo hankalin duniya akan irin mumunan hali da ukubar da ake ciki a wannan yankin.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Mar 02, 2017 11:16 UTC
  • Wakilan MDD Na Ziyara A Yankin Tafkin Chadi

Wata tawagar wakilan kwamitin sulhu na MDD na shirin soma wata ziyara yau Alhamis a yankin tafkin Chadi domin janyo hankalin duniya akan irin mumunan hali da ukubar da ake ciki a wannan yankin.

Yankin tafkin Chadi dai na cikin bukatar agajin gaggawa sakamakon tarin matsalolin mafi muni da ake fama dasu da suka hada da fari, hare-haren mayakan 'yan ta'adda, canjin yanayi da kuma rashin iya tafiyar da mulki na gari.

Wadanan jerin matsalolin sun shafi kimanin mutane Milyan 21 a kasashen da suka hada da najeriya, Chadi da kamaru da kuma NIjar.

Ziyara ta wakilan 15 zata taimaka wajen duba hanyoyin da MDD zata bi wajen shawo kan wannan matsala, duba da yadda MDD ta jima tana nuna halin ko in kula akan irin ukubar da jama'ar yankin suka shiga sakamakon matsalar Boko Haram a cewar jakadan Biritaniya a MDD  Matthew Rycroft.