Sakataren Janar Na MDD Zai Ziyarci Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18216-sakataren_janar_na_mdd_zai_ziyarci_kenya
Babban sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, zai fara wata ziyarar aiki gobe Lahadi a kasar Kenya.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 04, 2017 07:11 UTC
  • Sakataren Janar Na MDD Zai Ziyarci Kenya

Babban sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, zai fara wata ziyarar aiki gobe Lahadi a kasar Kenya.

A wannan ziyara Mista Guterres zai tattaunawa da wakilan gwamnatin kasar ta Kenya akan batutuwa da dama ciki har da halin da yankin ke ciki, kamar yadda kakakinsa ya fada a jiya Juma'a.

Kasar Kanya dai na makoftaka da kasashe irinsu Sudan da Tudu da Somaliya wadanda ke fama da matsalar fari wace ta shafi kusan mutane Miliyan uku.

Mista Guterres wanda ka kama jagorancin hukumar ta MDD a watan Janairun wannan Shekara, na tunanin fiddo da wasu hanyoyi na ganin bayan rikicin shekaru uku da ya dai-daita jinjira kasar ta Sudan ta Kudu.