An Cafke Masu Alaka Da Da'eh 15 A Marocco
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18600-an_cafke_masu_alaka_da_da'eh_15_a_marocco
Hukumomi a kasar Marocco sun sanar da cafke mutane 15 da ake zargi da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta da'esh.
(last modified 2018-08-22T11:29:49+00:00 )
Mar 18, 2017 05:52 UTC
  • An Cafke Masu Alaka Da Da'eh 15 A Marocco

Hukumomi a kasar Marocco sun sanar da cafke mutane 15 da ake zargi da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta da'esh.

An dai cafke mutanen ne a wasu yankunan kasar goma, kuma ana zarginsu da shirin kai hare hare a wasu mayan cibiyoyi na kasar.

Sanarwar da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar ta ce mutanen sun shirya kai hare-hare a wuraren shakatawa na jama'a da kuma ma'aikatun gwamnati a biranen da suka hada da Casablanca, Marrakech da Tanger.

Ma'aikatar ta ce tuni wasu daga cikin mutanen wanda galibi matasa suka fara samar da wasu kayayaki na hada abubuwa masu fashewa.

Kana kuma a cewar sanarwar wasu daga cikinsu suka nemi mallakar bindigogi wadanda zasuyi amfani dasu wajen kashe wasu mayan jami'ai.

za'a dai gabatar da masu zargin gaban alkali bayan gudanar da bincike.